Kano Ta Dabo Ci Gari

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kano


Shiga Masarauta ko Jaha


Gabatarwa

Kano, suna ne na birni daga cikin biranen Ƙasar Hausa na asali wanda kuma shi ne mafi albarka a cikinsu. Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya ce: “Kuma mafi albarkarta, Kano”. Sannan kuma sunan masarauta ne daga cikin manya-manyan masaratun Ƙasar Hausa da ma baki ɗayan Najeriyar wannan zamani da muke ciki. Bayan haka ma kuma ya taɓa zama sunan lardi a zamanin Turawan Mulkin Mallaka. Daga ƙarshe kuma Kano ce jaha mafi yawan jama’a a duk faɗin Tarayyar Najeriya.

Wannan gari mai suna Kano, shi ne fadar Masarautar Kano, cibiyar tsohon Lardin Kano sannan kuma matsugunnin fadar gwamnatin jahar Kano.

Cibiyar Kasuwanci, shi ne taken da gwamnatin Najeriya ta karɓa a hukumance. Wannan suna kuwa ba jayayya a cikinsa. Kano ce garin da yake da kasuwannin ƙasa-da-ƙasa sama da goma a iya cikin ƙwaryar garin. Abin da ya bai wa garin cikakkiyar damar taka muhimmiyar rawa a fannin kasuwanci tun shekaru sama da ɗari shida da suka shuɗe a faɗin duniya.

Idan ma ka ga dama, kana iya cewa kasuwanci ne ya kafa garin Kano. Kasuwar Kurmi, wacce ta haura shekaru ɗari shida tana wanzuwa a Kano, kasuwa ce wacce ba za a taɓa raba tarihinta da tarihin kafuwar garin Kano ba. Tun zamanin da su Dala suke farauta masunta kuma suna kamun kifi a yankin kurmin Jakara wanda kasuwar ta samo suna daga kurmin da mutane suke zuwa suna gudanar da kasuwanci irin na wancan zamanin ta hanyar bayar da abubuwan da suka samu su kuma su karɓi kifi da nama daga hannun masunta da mafarauta. Inji Sarkin Kasuwar Kurmi, Alhaji Abdullahi Maikano Darma a tattaunar da muka yi da shi a ranar 15, ga watan Janairu, 2019.


Yankin Kurmin Jakara Daga Kwarin Kwana Gayawa

Haka nan ma ta fuskacin sana’a da masana’antu, ba a bar Kano a bayan ba saboda gudunmawar da ta bayar wajen fitar da ingantattun kayayyakin da suka shafi fata da kuma saƙe tun ƙarnoni biyar da suka shuɗe. Kano ta yi fice a duniya a wancan zamani ta fuskar sana’o’in da suka shafi ƙira, jima, rini, saƙa da sauransu. Fitaccen marubucin tarihin Afirka, Rodney (1972), ya ce: “Ta ɓangaren Afirka ta Arewa, Turawa suka san jar jemammiyar fata mafi inganci wacce ake yi a Afirka, wacce aka yi wa laƙabi da Morocco Leather. A taƙaice wannan ƙwararru daga Hausa da Mandiga a Arewacin Najeriya da Mali su suke jeme ta sannan su rina ta”. Ni kuma na tabbatar maka da cewa, Hausa a nan, yana nufin garin Kano. Saboda su mutanen Mali su suka zo da jima Kano. Duba Sana’ar Jima.

Haka nan ta fuskacin addinin Musulunci da kuma karatun Alƙur’ani, Kano tun sama da shekaru ɗari shida aka buɗe makarantu da masallatai a dukkan faɗin masarautar.

Kano ita ce maƙyanƙyasar karatu da rubutun bokon dukkan faɗin Ƙasar Hausa ko kuma a ce Arewacin Najeriya kai tsaye. Gidan Ɗanhausa, shi ya zama matsugunnin makarantar fimare ta farko da ta yi nasarar yaye ɗaliban da suka yaɗa ilimin boko a dukkan Arewacin Najeriya.

Siyar Najeriya, wacce aka samu nasarar kafa jamhuriyar farko da ita, kuma jama’iyyun suka zama tubalin ginin fafutikar samun yancin kan ƙasa, an hafi wasu da yawa a Kano. Kusan mafiya yawan jama’iyyun Arewacin Najeriya ‘ya’ya ne ko jikokin NEPU da NPC waɗanda duk a Kano aka ƙyanƙyashe su.

Manufar wannan shafi da mai karatu yake karantawa, ita ce fito da duk wani abu da ya shafi Kano wanda hannunmu zai iya kai wa gare shi ta fuskancin tarihin garin, masarauta, sarakuna, bukukuwa, addini, jaha, kasuwanni, gwamnoni, limamai, mashahuran malamai, muhimman gurare, mashahuran attajirai da sauransu. Abin sani kawai shi ne ya kamata ka zama mai bibiyar wannan shafi domin samun sababbin bayanai da za a iya ɗurawa a kodawane lokaci. Ko kuma ka lalubi Rumbun Ilimi a shafin Fesbuk ka kuma yi ‘Like’, wannan za ta baka cikakkiyar damar samun masaniya game da sabunta duk ma shafin da muka yi nan take.

Manazarta:


Ballo M. (1974). Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur. Daarul Kutub, 1974.

Rodney W. (1972). How Europe Under Developed Africa. Bogle-L ‘Ouverture Publications, London and Tanzanian Publishing House, Dar-Es-Salam.

Tattaunawa da Abdullahi Maikano Darma, shugaban Kasuwar Kurmi a ranar 15 ga watan Janairu na shekarar 2019.

Yakasai T. (2004). Tanko Yakasai, The Story of a Humble Life, An Autobiography, Volume I. Government Printers, Kano-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub